Yadda aka gudanar da bikin ranar Alƙalai Mata ta Duniya
Mar 10 2025
10 mins
Shirin Rayuwata na yau ya yi duba ne kan bikin ranar Alƙalai Mata ta Duniya, wadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta samar a shekarar 2021 kuma ake gudanar da bikinta a ranar 10 ga watan Maris. Rahotanni dai sun nuna cewa mata na samun nasarorin a fannin shari'a, a daidai lokacin da ake hasashen samun adadin mata alƙalai da zai zarce maza nan da shekaru masu zuwa.